Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Yi Watsi Da Bukatar Tsohon Shugaban Brazil Fita Daga Kurkuku


Rashin sa’ar tsohon shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lulu da Silva ta kaucewa daurin shekaru 12 a gidan kaso na nufin watakila za’a daure shi nan bada dadewa ba, akalla mako zuwa, saboda wasu ka’idoji na tuhumar da ake masa kan cin hanci da rashawa.

Yau Alhamis Kotun kolin Brazil ta yanke hukuncin yin watsi da bukatar tsohon shugaban Brazil Luiz Inacio Lulu da Silva fita daga kurkuku yayin da yake daukaka tuhumar da ake masa ta cin hanci da rashawa.

Hukuncin da alkallai biyar cikin shida na kotun kolin suka yanke ya haifar da babban kalubale ga wannan dan takara da yake gaba a zaben shugaban kasa na wannan shekara a daya daga cikin manyan kasashen nahiyar Latin America.

Lula da magoya bayansa dai sun ce zargin da ake masa duk siyasa ce kawai, kuma yanzu haka rahottani sun ce hukumomin sun fara shirin daukar matakan fuskantar manyan tarukkan gangami da za’ayi a biranen kasar da dama na masu goyon bayan tsohon shugaban da masu kyamarsa.

An yankewa Da Silva hukunci a watan Yulin bara saboda ya taimakawa wani kamfanin ‘yan kwangila na masu gine-gine samun kwangiloli masu tsoka bayanda suka yi masa alkawarin bashi wani katafaren gida a bakin teku. Da Silva dai ya musanta zargin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG