Accessibility links

Kungiyar Cigaban Kananan Kabilun Arewacin Najeriya ta Goyi Bayan Taron Kasa


Gwamna Jonah Jang na jihar Filato

Yayin da kasar Najeriya ke shirin yin taron kasa kungiyar cigaban kananan kabilun arewacin Najeriya ta jaddada goyon bayanta ga taron

Kungiyar cigaban kananan kabilun arewacin Najeriya ta yi alkawarin bada gudunmawarta wajen cigaban Najeriya a wurin taron kasa da ake shirin gudanarwa.

Shugaban kungiyar Mark Amani yace kananan kabilu dake arewacin Najeriya sun bada gagarumin gudunmawa wajen hadin kan Najeriya a matsayin tsintsiya madaurinki daya. Dalili ke nan suke bada goyon baya domin tattauna matsalolin da suka addabi arewacin Najeriya. Yace sun goyi bayan a yi taron domin akwai abubuwa da yawa da kananan kabilun arewa suka rasa.

Lokacin da aka yi yakin basasan Najeriya sojojin da suka yi yaki kusan kashi casa'in da biyar daga kananan kabilun arewa suka fito. Mark Amani yace amma abun mamaki yau za'a yi abu a arewa amma babu kananan kabilun arewa ciki. Yace babu ruwansu da batun addini domin sai a shiga gida daya a tararda 'yan uwa daya uba daya amma akwai Musulmi da Kirista da ma mai bin addinin gargajiya cikinsu. Yace to ta yaya zasu tunkari 'yanuwansu da bala'i.

Mark Amani ya kara da cewa su babu ruwansu da batun addini. Sarakunan yankinsu da Musulman da Kiristan su tabbatar da cewa idan suna son su yi adalci idan ana taron sarakuna su dinga zuwa domin cigaban al'umominsu. Idan kuma gwamnatin Najeriya ce take hanasu ko wasu daban to a yi gyara .

Tsohon kwamishanan yada labarai na jihar Filato Mr. Gideon Barde yace su ne tsakiyar Najeriya wato su ne suka hada kasar. Yace koda wasu sun balle sun tafi su zasu rike Najeriya. Yace ba zasu taba yadda da wadanda ke neman wargaza Najeriya ba. Yace komene addinin mutum ko kabila bai kamata ana kashe kashe ba domin mahalicci daya ne.Yace wannan ba komi ba ne illa jahilci ko kuma cuta ce dake bukatar warkaswa. Yace su mutanen arewa ne amma an barsu a baya sosai.

Ga rahoto.

XS
SM
MD
LG