Accessibility links

'Yanbindiga Sun Sake Kai Hari Jihar Adamawa


'Yan gudun hijira daga hare-heren ;yanbindiga a arewa maso gabas

Kwana kwanan nan 'yanbindiga suka kashe mutane fiye da dari da ashirin a Izhige jihar Borno wadda ke makwaftaka da jihar Adamawa sai gashi ita ma jihar Adamawa an kai mata hari

Rahotanni daga yankin Gombi a jihar Adamawa na nuni da cewa wasu 'yanbindiga sun sake kai hari a kauyen Garga cikin gundumar Ganda inda suka kashe mutane goma sha daya.

Shaidun gani da ido da shugabannin al'umma sun tabbatar da harin. Sun ce mutane da dama sun kauracewa gidajensu domin tsoron kada suma a rutsa da su. Wasu ma har kan duwatsu suka hau domin samun tsira. 'Yanbindigan wai har kudi suke ta neman a basu yayin da suke kashe mutane. Ganau sun ce 'yanbindigan na sanye da kayan soja.

'Yansanda a jihar sun tabbatar da harin. Amma domin ana cikin dokar ta baci kuma sojoji ne ke kula da harkokin tsaro dole wakilin Muryar Amurka ya nemi ya tuntubi sojojin. Kokarin samun kakakin sojojin Keften Jafaru Nuhu domin karin bayani ya cutura.

Ga rahoto.
XS
SM
MD
LG