Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar ISIS Na Ci Gaba Da Rasa Yankunan Dake Karkashinta A Iraqi Da Syria


ISIS
ISIS

Wata cibiyar bincike mai zaman kanta a Ingila da ake kira IHS tace kungiyar ISIS tana kara hasarar yankunan da ada suke karkashinta a Iraqi da kuma Syria, kamar yadda cibiyar tayi bayani jiya lahadi.

Cibiyar IHS tace ISIS ta rasa kashi 12 cikin dari na yankuna da take iko da su a watanni shida na farko na wannan shekara, kari kan kashi 14 da aka kwace daga hanunta a bara. Baki daya, cibiyar tace, ISIS ta rasa murabba'in kilomita 68,300 na kasa a kasashen biyu a bara.


Kungiyar tayi wannan rashin ne sakamakon matsin lamba daga dakarun Syria da suke samun taimakaon daga jiragen yakin Rasha, da kuma mayakan sakai na kurdawa wadanda Amurka take daurewa gindi.

A Iraqi kuma, sojojin kasar wadanda Amurka take taimakwa da jiragen yaki, suka ta rasa biranen Ramadi da Fallujah, duk da cewa har yanzu kungiyar tana rike da babban birnin Mosul.


Amma duk da haka, kungiyar ta kaddamar da munanan hare hare da bama-bamai a Bagadaza, da Paris, da Brussels,haka ta tunzara wasu kai hare hare a wasu sassan turai da kuma Amurka.

XS
SM
MD
LG