Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Mata A Jamhuriyar Nijer Sun Taya Dr. Ngozi Murna


 Dr Ngozi Okonjo-Iweala
Dr Ngozi Okonjo-Iweala

Masana sha’anin tattalin arziki da kungiyoyin kare hakkin mata a jamhuriyar Nijer sun yi na’am da matakin jaddada tsohuwar ministar kudin Najeriya Dr. Ngozi Okonjo Iweala a matsayin sabuwar shugabar hukumar cinikiyya ta duniya.

Tabbatar da ita ya biyo bayan janyewar da abokiyar hamayyarta wato ministar kasuwancin Korea ta Kudu Yoo Myung Hee ta yi a wannan fafatawa. Kungiyoyin matan snu shawartar Dr. Ngozi kada ta manta da gida Afrika.

A ranar Litinin din da ta gabata ne Dr. Ngozi ta karbi ragamar shugabancin hukumar cinkayya ta duniya sakamakon cikakken goyon bayan da ta samu daga sabuwar gwamnatin Amurka karkashin jagorancin shugaba Joe Biden.

Tsohuwar ministar kudin tarayyar Najeriya wacce ta rike mukamai da dama a gida da waje Dr. Ngozi ita ce mace ta farko kuma ‘yar Afrika ta farko dake shugabancin hukumar ta WTO dalili ke nan da yasa kungiyoyin kare hakkin mata a jamhuriyar Nijer ke alfahari da ita inji Hajiya Halima Sarmeye mataimakiyar shugabar kungiyar SOS FEVVF.

“Yau ranar farin ciki ne ga mata na duniya baki daya ba Najeriya kadai ba. Bakar fata ba babu ilimi ko basira ko hikima bane, matsalar ita ce banbancin launin fata da ake sakawa cikin rayuwa ke kawo cikas. Harkokin kula da iyali sune su kan hanawa mata yin wasu ayyuka amma ba wai dan ba ilimi ba,” Inji Halima Sarmeye.

Haka Shi ma masanin tattalin arziki Dr. Soly Abdoulaye ya yi farin ciki da zaben Mme Ngozi a wannan matsayi. Ya ce abin jin dadi da farin ciki da alfahari ne ga dukkan mu ‘yan Afrika ganin Dr. Ngozi ta dare a kan wannan kujerar shugabancin kasuwancin duniya.

Ya kuma kara da cewa damka ragamar wannan hukuma a hannun wata 'yar Afrika alheri ne ga nahiyar Afrika wace ta jima tana fuskantar rashin adalci daga masu bakin fada aji a duniya inji shi.

A farkon shekarar nan ta 2021 kasashen Afrika sun kaddamar da tsarin kasuwancin maras shinge sabili da haka masanin tattalin arziki Dr Soly Abdoulaye ke cewa kamun ludayin Dr N’gozi Okonjo Iweala na iya zama wata hanyar karfafa wannan yarjejeniya.

Saurari rahoton Souley Moumouni Barma cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

Karin bayani akan: Ngozi Okonjo-Iweala, WTO, Nigeria, da Najeriya.

XS
SM
MD
LG