Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ngozi Okonjo-Iweala Ta Kira Nadin Ta Mai Cike Da Tarihi


Ngozi Okonja-Iweala.

A wani lamari mai cike da tarihi, Kungiyar Kasuwanci ta Duniya ta zabi mace ta farko kuma 'yar Afirka ta farko da za ta jagoranci kungiyar.

A jiya Litinin ne wakilai daga kasashe 164 da suka hada da kungiyar ta WTO suka nada masaniyar tattalin arzikin Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala, mai shekara 66, a matsayin darakta-janar na kungiyar.

Okonjo-Iweala ta fada yayin wani taron manema labarai ta yanar gizo a ranar Litinin cewa, ta himmatu don fara aikin sake fasalin kungiyar tare da zamanantar da dokoki don kawo su har zuwa matsalolin karni na 21.

Ta ce "Ina godiya da amincewar da kuka yi min ba kawai a matsayi na na mace da 'yar Afirka ba, har ma da ilimi na da gogewata kuma, kamar yadda wasunku suka fada, ina da karfin gwiwa da sha'awar yin aiki tare da ku don aiwatar da sauye-sauye masu yawa da kungiyar WTO ke bukata a nan gaba, ”

Ta ce daya daga cikin manyan abubuwan da ta sanya a gaba shi ne mayar da hankali kan batun COVID-19, gami da yin aiki tare da cibiyoyin COVAX da na ACT don gaggauta samar da kayayyaki da alluran rigakafi ga kasashe matalauta.

Karin bayani akan: Ngozi Okonjo-Iweala, WTO, Nigeria, da Najeriya.

XS
SM
MD
LG