Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kura Ta Lafa Bayan Wani Rikici Da Ya Barke A Wata Kasuwar Legas


Sufeto-Janar na 'yan sandan Najeriya, Ibrahim K. Idris
Sufeto-Janar na 'yan sandan Najeriya, Ibrahim K. Idris

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta bada sanarwar kama wasu mutane biyar sakamakon rikicin da ya auku a wata kasuwa da ke jihar, haka kuma mutane hudu sun samu raunuka a wannan fada tsakanin Hausawa da Yarbawa.

Fadan da ya kaure tsakain matasan Yarabawa da Hausawa da ya yi dalilin jikata mutane da dama, ya so ya rikide ya zama fadan kabilanci, wanda a cewar masana lamarin ka iya yin muni idan ba a dauki mataki da wuri ba.

A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar ta Legas, ta hannun kakakinta, DSP Bala Elkana, ta ce mutane hudun da aka kama ana gudanar da bincike a kansu, kuma da zarar an kammala binciken za'a gurfanar da su a kotu.

DSP Bala ya ce an fara fadan ne tsakanin mutum biyu a wata kasuwar da ke Okeruwa ta shiyar Alumosho, lamarin da ya rincabe bayan mutane biyun sun samu goyon baya daga ‘yan kabilansu.

Sai dai bangaren Hausawa ya ce akasarin wadanda aka kaman Hausawa ne, a yayin da aka kyale 'yan bangaren abokan fadansu, zargin da rundunar ‘yan sanda ta ce tana bincike a kai.

Babangida Jibrin ya aiko mana da rahoto daga Legas:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG