Accessibility links

Lahadi,Sha Biyar Ga Watan Disamba Aka Shirya Yin Jana’izar Mandela a Garin Haihuwarsa


Za’a fara tarukan yin addu’a domin tunawa da marigayi Nelson Mandela a ran Talata a babban filin wasan tamaulan birnin Johannesburg.

Hukumomin Afirka ta kudu sun bada sanarwar cewa za’a gudanar da Jana’izar Nelson Mandela a ran Lahadi sha biyar ga watan Disamba a garin haihuwarsa na Qunu.
Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta kudu ne yayi bayanin dalla-dallar shirye-shiryen jana’izar da ta ahada da dukkan matakan da Gwamnatin Afirka ta kudu ke dauka domin gudanar da addu’o’in girmama marigayi Mandela, tsohon shugaban Afirka ta kudu ran Juma’ar da aka ware domin al’ummar Afirka yin addu’o’I na musamman da tunawa da tsohon shugaban kasarsu.

Mr. Jacob Zuma ya ayyana lahadin nan mai zuwa ta zama ranar yin addu’o’i domin tunawa da marigayi Mandela inda za’a yi addu’o’i a masallatai da Mujami’u da sauran wuraren taruwar jama’a da gidajensu. Sannan shugaban na Afirka ta kudu yayi kira ‘yan Afirka ta kudu da suyi koyi da halin zaman rayuwar marigayi Mandela.
XS
SM
MD
LG