A ranar Asabar da ta gabata Korea ta Arewa ta yi wani gwajin makami mai linzami da bai yi nasara ba a tungar sojin ruwanta dake Sipo a gabashin gabar tekun kasar, jerin gwaje-gwajen makaman na baya sun sabawa sharudojin takunkumin da MDD ta kakaba mata.
A wata sanarwa ta bai daya, wakilai a Kwamitin sulhun MDD sun bayyana matukar damuwarsu game da halayyar Koriya Ta Arewa na tada rikici da takala tare da bayyana rashin da’a ga tanajin takunkumi da MDD ta kakaba mata.
Mambobin Kwamitin sulhun sun amince baki daya, Kwamitin ya ci gaba da lura da halin da ake ciki tare da daukar muhimman matakai har da takunkumi bisa kokari da Kwamitin ke yi tun farko a cewar sanarwar.
Sanarwar ta ce Kwamitin sulhun zai yi marhaban da kokarin kasa da kasa na samar da hanyar warware wannan lamari cikin kwanciyar hankali da kuma tattaunawa.
Facebook Forum