Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lukaku Ya Isa Italiya Don A Duba Lafiyarsa, A shirinsa Na Komawa Inter Milan


Romelu Lukaku a shekarar 2018.
Romelu Lukaku a shekarar 2018.

A watan Agustan bara, Lukaku ya sake komawa Chelsea akan kudi dala miliyan 118.

Dan wasan Chelsea, Romelu Lukaku ya isa birnin Milan na kasar Italiya don a duba lafiyarsa gabanin ya kammala shirinsa na komawa kungiyar Inter Milan a matsayin dan wasan aro.

A lokacin da Lukaku ya isa, magoya bayan kungiyar ta Inter Milan sun yi ta murna inda suka yi ta kiran sunansa yayin da shi kuma ya dago musu hannu ta tagar ginin da za a duba lafiyarsa.

A watan Agustan bara, Lukaku ya sake komawa Chelsea akan kudi dala miliyan 118.

Sai dai tauraronsa bai haska ba tun bayan komawarsa kungiyar, inda ya zura kwallaye takwas kacal a gasar Premier League.

Yanzu Lukaku, dan shekara 29, wanda dan asalin kasar Belgium ne, ya dawo Inter inda ya zura kwallaye 64 a wasanni 94 a tsakanin kakar wasanni ta 2019-21.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG