Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lula da Silva Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa A Brazil


Lula da Silva zagaye da magoya bayansa a Brazil
Lula da Silva zagaye da magoya bayansa a Brazil

Wannan shi ne karon farko da shugaba mai ci ya fadi zabe a siyasar kasar ta Brazil.

Tsohon shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva, ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a ranar Lahadi.

Da Silva ya samu sama da kashi 50.9 na kuri’un da aka kada a zaben da aka yi a zagaye na biyu yayin da abokin hamayyarsa kuma Shugaba mai ci Jair Bolsonaro ya samu kashi 49.1.

Wannan zabe shi ne mafi zafi da kasar ta Brazil ta fuskanta tun bayan da ta koma kan turbar dimokradiyya a shekarar 1985.

Kazalika wannan shi ne karon farko da shugaba mai ci ya fadi a zabi a tarihin zaben kasar.

A shekarun baya wata kotu ta taba yankewa da Silva hukuncin zaman gidan yari na tsawon kwanaki 580, bayan da aka same shi da laifin halalta kudaden haram.

Sai dai daga baya wata babbar kotu ta soke hukunci saboda an zargi wancan alkalin da nuna bangaranci.

Hakan ya ba da Silva mai shekaru 77, damar sake tsayawa takara mukamin shugaban kasa a karo na shida.

A ranar 1 ga watan Janairu za a rantsar da shi. Ya yi mulkinsa na farko tsakanin 2003 zuwa 2010.

XS
SM
MD
LG