Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Magajin Garin Sokoto Hassan Ahmad Danbaba Ya Rasu


Magajin Garin Sokoto Hassan Ahmad Danbaba
Magajin Garin Sokoto Hassan Ahmad Danbaba

Dangin Magajin garin Sokoto Hassan Ahmad Danbaba sun tabbatar da rasuwar sa ranar Asabar bayan gajeruwar rashin lafiya.

Sarkin Rafin Gumbi Sama'ila Abdulkadir Mujeli, wanda kane ne ga marigayin kuma shi ne ke rike da rasautar Gumbi, shi ne ya tabbar da rasuwar Hassan Ahmad Danbaba.

Danbaba dai ya rasu ne a asibitin sojoji na 44 Battalion da ke Kaduna.

Sarautar magajin gari na daga cikin manyan sarautu a majalisar kolin mai alfarma Sarkin Musulmi, wadanda ke zaben Sarkin Musulmi idan sarautar ta fadi.

Hassan Ahmad Danbaba, wanda jika ne ga firimiyan arewa Sardaunan Sokoto Ahmadu Bello, ya gaji sarautar Magajin gari kaka-da-kakanni tun daga Magaji Dan Jada, wanda sarkin musulmi Muhammad Bello ya nada bayan wafatin Shehu Usmanu Dan Fodiyo.

Yanzu dai dangin marigayin na kan shirye-shirye na kai gawar Sokoto da kuma Jana'izar sa.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG