Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahathir Na Niyar Murabus Ya Bawa Tsohon Mataimakinsa Dama


Anwar Ibrahim
Anwar Ibrahim

Tsohon mataimakin Firai Ministan Malaysia Anwar Ibrahim ya karfafa dawowarsa a cikin harkokin siyasar kasar, inda ya yi nasara a zaben majalisar dokokin kasar a jiya Asabar.

Sake samun kujerar majalisar ya kara kusanta dan shekaru 71 da haifuwa ga babban mukamin kasar, saboda Firai minista Mahathir Mohamad mai shekaru 93 yace zai yi murabus shekaru biyu masu zuwa domin ya baiwa Anwar dama ya gaje shi.

Anwar dai shine mataimakin Firai Ministan kasar a lokacin mulkin Mahathir na baya, har izuwa lokacin da aka kore shi a kan wannan mukami a shekarar 1998. Daga bisani an yanke masa hukuncin dauri a kan laifukan cin hanci da rashawa da kuma luwadi, laifukan da shi da magoya bayansa suka ce an dora masa ne domin gamawa dashi a siyasance. Bayan wani lokaci an janye laifukan kuma aka masa afuwa.

Anwar da Mahathir sun sake yin wani hadin gwiwa suka bawa Najib Razak da jami’iyarsa ta Barisan Nasional Coalition kashi a zaben farkon wannan shekara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG