Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahaukaciyar Guguwa Ta Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane Biyu A Philippines


<strong>قرار است انتخابات ریاست جمهوری ششم میزان در ۴۹۰۰ مرکز رای&zwnj;دهی برگزار شود</strong>
<strong>قرار است انتخابات ریاست جمهوری ششم میزان در ۴۹۰۰ مرکز رای&zwnj;دهی برگزار شود</strong>

Jami’ai sun ce, Kusan mutane biyu ne suka mutu sakamakon Mahaukaciyar guguwar Nock-Ten, wacce ta birkita shagulgulan kirsimeti a wani sashi na kasar Philippines, guguwar da ta saukar da Iska da Ruwa a Manila a yau Litinin.

Guguwar ta fantsamo ne da yammacin Lahadi a wani kebabben tsibiri na Catanduanes da iska mai gudun kusan kilomita 255 cikin sa'a guda.

Jami’an yanayi sunce, duk da guguwar ta sassauta a yau Litinin, har yanzu tana dauke da iska mai gudun kilomita 130 (wato mil 80) cikin sa'a guda da kuma kilomita 215 (wato mil 133) cikin sa'a guda.

Yan sanda sun bada rahoton wasu ma’aurata biyu da suka mutu sakamakon ruwa da ya tafi dasu a lardin Alby dake Kudancin Manila.

Jami’an gwamnatin masu kula da harkokin yanayi sunce, guguwar da mutanen garin ke kira Nina, ta kada zuwa Arewa maso Yammaci a tafiyar kilomita 20 cikin sa'a guda, inda ake tsammanin zata isa Manila a yau sannan ta fita ta Kudancin Kogin Sin da yammacin yau Litinin.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG