A Jiya Laraba ya kamata mambobin wannan kwamitin su kada kuri’a, amma kuma ‘yan bangaren Democrat suka janye daga halartar zaman.
Hakan kuma suka yi a lokacin da kwamitin kudi zai tantance Steve Mnuchin a matsayin Sakataren baitul malin Amurka da kuma Tom Price a matsayin wanda aka zaba ya jagoranci Ma’aiaktar kiwon lafiya da harkokin jama’a.
Dokar majalisar Dattawan Amurka ta tanadi cewa lallai sai an samu akalla mutum guda daga bangaren marasa rinjaye a majalisar kafin a kada kuri’a.
Sai dai Sanata Orrin Hatch na jihar Utah dake jagorantar kwamitin na kudi, wanda kuma ya nuna fusatarsa a fili, ya yi jagoranci sauya wannan doka, wanda hakan kuma ya sa ‘yan Republican zalla suka samu damar kada kuri’ar amincewa da Mnuchin da kuma Price.
Su dai ‘yan majalisar Dattawa a bangaren ‘yan Democrat, sun ce suna bukatar karin lokaci kafin su shiga aikin tantance mutanen da shugaba Donald Trump ya mikawa majalisar domin neman amincewarsu.