Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya zata Maye Gurbin Jam'inta Da Aka Kora A Somalia


Antonio Guterres, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ya fada a jiya Juma’a cewa ya yi matukar bakin ciki da shawarar korar babban jami’in Majaisar Nicholas Haysom daga kasar Somalia wanda gwamnati tarayyar kasar ta dauka, amma kuma yace zai tura wani a madadinsa.

Babban sakataren MDD yace ya tabbatar da Mr. Haysom nada kwarewa kuma mutum ne mai daraja wanda ya yi aikin hukuma a matsayin kasa da kasa, wanda kuma ya taka rawar gani a shugabanci a wurare da dama da ma helkwatan MDD, inji mai magana da yawun Antonio Guterres a jiya Juma’a. Sai dai babban sakataren yace har yanzu zai ci gaba da bada himma a kan bukatun mutanen Somalia a cikin ayyuakan da Majalisar keyi a Somalia.

Gwmnatin Somalia ta ayyana babban wakilin MDD Haysom a matsayin wanda bata kaunarsa a cikin kasar tun ranar farkon wata Janiru kuma ta umarce shi da bar kasar bayan watanni hudu kacal da ya fara aiki a matsayin wakilin babban sakataren MDD na musamma kuma ya shugabanci ofishin Majalisar a wannan kasa.

Gwamnatin ta nuna fushinta a kan wata wasika da Haysom ya aikewa hukumomin kasar inda ya tado da batun tsohon shugaban kungiyar al-Shabab Mukhtar Robow wanda ya shiga siyasa kuma ya bayyna aniyarsa ta shiga takarar zabe da za a gudanar a yankin kudu maso yammacin kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG