Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Kenya Ta Yi Waje Da Jaririn Wata Biyar


Zauren Majalisar Dokokin kasar Kenya
Zauren Majalisar Dokokin kasar Kenya

A ranar Laraba da safe ne aka yi ta tada jijiyar wuya a zauren majalisar dokokin kasar Kenya bayan da wata ‘yar majalisa Zuleika Hassan ta shiga zauren majalisar da jinjirin wata biyar.

Shigar ‘yar majalisar da danta zauren majalisar ya sa zaman majalisa ya tsaya cak, yayinda ‘yan majalisa da dama suka bukaci su fice daga majalisar.

“Ranka ya dade kakakin majalisa, wani bako ya shigo wannan majalisar, kuma haka bata taba faruwa ba tun shekara ta dubu da dari tara da sittin da uku. Mai Girma Kakaki, wannan wulakanta majalisa ne, kuma ya kamata a tuhume ta da aikata ba daidai ba. Tilas ne mu kare mutuncin wannan majalisar.

Mukaddashin kakakin majalisar Chirstopher Omulele ya yanke hukumci cewa, abinda ‘yar majalisar ta yi bai dace ba sabili da haka ya umarci gagarabadau na majalisar ya fitar da ita daga zauren.

Duk ya yake tana son ta kula da jaririnta, wannan ba wurin da zata kula da shi bane, saboda haka na umarce ta da ta fice ba tare da bata lokaci ba ta dawo idan ta ajiye shi a wani wuri.

A nata ra’ayi, Saida Ali wata ‘yar gwaggwarmayar kare hakkin bil’adama ta kasar Kenya tace abinda kakakin ya aikata ne ba daidai ba.

Misali ke nan dake nuna cewa, wadansu suna gani bai kamata mata su shiga wadansu wurare ba, ko rike wadansu mukaman shugabanci, ko kuma suna gani wadansu cibiyoyin da ake tsaida shawarwari ba wurin shigar mata bane. Wannan babbar matsala ce a wurina, sabili da kuwa muna ci gaba da nuna cewa maza sune suke da iko muna kara basu damar rufewa mata baki.

Da take hira da manema labarai bayanda aka fitar da ita daga zauren majalisar. Zuleika tace an bata zabi biyu ranar Laraba ko dai ta zo aiki da jaririn, ko kuma kada ta zo baki daya, ta kuma gwamnace kada taje aikin.

A shekarar dubu biyu da goma sha bakwai, majalisar dokokin kasar Kenya ta amince da kudurin da ya bukaci ma’aikatu su samar da wuraren da mata masu shayarwa zasu iya kula da ‘ya’yansu. Sai dai kamfanoni kalilan ne kawai suka yi wannan tanadin.

Ga dai fasarar wakiliyar Muryar Amurka Rael Ombuor daga birnin Nairobi:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:29 0:00
  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG