Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilan Amurka Ta Tabbatar Da Shirin Tallafin Coronavirus Saura Ta Dattawa


Shugaba Biden.
Shugaba Biden.

A yau Asabar shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar da jawabi a kan shirinsa na dala triliyan daya da biliyan 900 na tallafin COVID-19 da majalisar wakilai ta tabbatar da shi da safiyar yau.

Biden zai tattauna a kan shirin ceto Amurkawa a fadar White House kafin ya tashi zuwa jiharsa ta asali ta Delaware domin hutun karshen mako.

Shirin kashe kudin, dake zai tallafawa ayyuka da gwamnatoci da kuma miliyoyin Amurkawa da matsalolin coronavirus ya yi mummunar tasiri a kansu, yanzu za a mika shi zuwa majalisar dattawa domin kada kuri’a akai.

Kamar yanda aka zaci, masu rinjayi sun samu kuru’u 219 na wadanda suka amince da shirin a kan kuru’u 212 na wadanda basu ra'ayi, a kuri’ar da aka kada a majalisar wakilai mai rinjayin Democrat, lamarin dake zama nasarar farko da Biden ya samu a majlisa tun lokacin da ya zama shugaban kasa a ranar 20 ga watan Janairu.

Yawancin ‘yan Republican sun kalubalanci wannan matakin da zai dauki nauyin kudin rigakafi da kuma kudin kayan jinya na yaki da annobar COVID-19 da ta hallaka sama da mutum dubu 580 a Amurka kana tasa wasu miliyoyi suka rasa ayyukansu.

Wannan tallafin zai kuma bada damar biyan karin dala 1,400 ga daidaikun Amurkawa da kuma taimakon kudi na gaggawa ga iyalai da kananan ayyuka da gwamnatocin kananan huumomi da na jiha.

XS
SM
MD
LG