Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mambobin Majalisar Dinkin Duniya A Yemen Sun Koka Akan Yanyin Kasar


Mambobin kwamitin majalisar dinkin duniya na ci gaba da nuna damuwarsu akan irin yanyin da jama'a ke ciki a Yemen, lamarin da suke ganib zai haifar da fargaba mai tsanani.

Mambobin kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya, sun nuna damuwar su akan yanayin da ake ciki a Yemen, kwana guda a bayan da 'yan tawaye suka hallaka tsohon shugaban kasar kuma tsohon abokin kawancensu Ali Abdallah Saleh, biyo bayan barkewar rikici a sakamakon wargajewar kawancensu.

Jakadan kasar Faransa a Majalisar dinkin duniya, Francois Delattre, ya ce “yanayin da Yemen ke ciki a yanzu zai haifar da lokaci mai cike da hatsarin gaske a fagen daga, haka kuma ga ayyukan jinkai a cikin kasar."
Ya kara da cewa burin mu na farko shine mu dakatar da fadan da ake gwabzawa

yanzu ta hanyar tsagaita wuta, mu kuma samar da ayyukan jinkai ga dukkan 'yan kasar Yemen, ta dukkan tashoshinta na ruwa da kuma filayen saukar jiragen samanta.

Biyo bayan mutuwar Saleh, dan shi Ahmed Ali ya sha alwashin yin fito na fito da ‘yan Houthi masu samun goyon bayan kasar Iran.
A wata sanarwa Ali ya bayyana cewa zai yi fito na fito da makiyan bil’adama da kuma kasa, da suke neman wargaza
kasa da samunta da kuma cin zarafin ‘yan kasar Yemen da kuma kasar

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG