Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Gargadin Mayar Da Birnin Kudus Babban Birnin Isra'ila


Yayin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ke kokarin fitar da wata sanarwa akan kasar Isra'ila, kasashen Larabawa da Musalmai sun yi gargadin cewa sanarwar ka iya dagula kokarin da amurka ke yi na wanzar da zaman lafiya tsakanin kasashen da Isra'ila.

Shugaba Donald Trump na bugawa shuwagabannin gabas ta tsakiya da dama waya kafin a fitar da wata sanarwa , watakila zuwa gobe laraba, kan cewa Amurka zata amince da birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila.

Sanarwa daga fadar white House ta bayyana cewa shugaba Trump na tattaunawa da Fiyani Ministan Isra’ila Benjamin Natanyahu, da shugaban palasdinawa Mahmoud Abbas da kuma sarkin Jordan Abdallah, da safiyar yau, zai kuma kira sauran shuwagabannin yankin daga baya.

Babu wata takamaimiyar Magana data fito daga white house akan tattaunawar amma kafar yada labaran Palasdinu, ta bada rahoton cewa shugaba Trump, ya ba Abbas tabbacin fitar da sanarwa akan birnin kudus na tafe.

Kasashen larabawa da na Musulmi sun yi gargadin fitar da sanarwar na iya bata kokarin da Amurka ke yi na cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Larabawa da kasar Isra’ila. Babban shugaban Paladinawa, Nabil Shaath, y ace baza a sake daukar shugaba Trump, a zaman mai shiga tsakani na gaskiya ba.
Shugaban Turkiyya, Rajab Tayyib Erdowan, yayi barazanar cewa zai tsinke hulda da kasar Isra'ila, muddin Trump ya amince da Qudus a zaman babban birnin Isra'ila.

Facebook Forum

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG