Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cafke Masu Garkuwa Da Mutane Akan Iyakar Najeriya Da Jamhuriyar Nijar


Dubun wadansu mahara masu garkuwa da mutane ta cika a garin Garu a karamar hukumar mulkin Illela ta jihar Sokoto da ke iyaka da Birni N'Konni a Jamhuriyar Nijar, yayin da wadansu suka kashe mutun guda a Araba dake da tazarar kilomita 2 da birni N'Konni.

Alhaji Mustafa Issa Garu Ciaman, yayi wa Muryar Amurka bayyanin cewa sun yi sa'ar cafke mutane 4 da suka so yin garkuwa da wani a garin Garu.

Daya daga cikin mutane 3 da ako sako, ya ce masu garkuwa da mutanen suna dauke ne da manyan bindigogi, har da masu sarrafa kansu, suka tafi da su kamin su sako shi.

Yanzu haka dai a wannan iyakar ta Nijer da Najeriya masu garkuwa da mutane na cigaba da sakin jiki su, suna kara mamaya ta hanyar kai hari a duk inda suke bukata a karamar hukumar mulkin Illela.

Saurari cikakken rahaton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00

Karin bayani akan: Muryar Amurka, Nijer​, Nigeria, da Najeriya.

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG