Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mataimakin Sakataren Majalisar Dikin Duniya Ya Ziyarci Sansanin 'Yan Gudun Hijira dake Nijar


Ban Ki-moon, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ko MDD

Stephen O'Brien mataimakin sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya kai ziyara sansanin 'yan gudun hijira dake Asaga cikin jihar Diffa a jamhuriyar Nijar kuma bayan ziyarar ya bayyanawa manema labarai abubuwan da ya tsinta kafin ya kama hanyarsa ta zuwa Najeriya

A taron manema labarai da Stephen O'Brien ya kira jim kadan bayan kammala ziyarar da ya kai a sansanin 'yan gudun hijira dake Asaga cikin jihar Diffa ya bayyana abubuwan da ya gano.

Yace mutanen da ya tattauna dasu a sansanin sun bashi labarai masu rikitarwa misali kamar wadanda suka shaida masa su mazauna Damasak ne a tarayyar Najeriya. Suka ce a wajejen karfe takwas na safe suna zaune sai 'yan Boko Haram suka shiga garinsu suka dinga kone gidajensu a lokacin da 'ya'yansu suke makaranta.

Ba tare da shiri ba suka tsallaka zuwa Nijar inda wasu mazauna Diffa suka tallafa masu da abinci da dai sauran kayayyaki. Saboda haka Stephen O'Brien yace ya zama wajibi a tuna da al'ummomin yankin Diffa a tallafin da mutane zasu ba wadanda rikicin Boko Haram ya daidaita.

Mutane kimanin miliyan biyu ne aka bayyana rikicin Boko Haram ya rutsa dasu a yankin Diffa yayinda aka kuma kiyasta mutane dubu dari biyu da arba'in da daya ne suka tashi daga matsugunansu na asali da suka hada wadanda suka ketaro daga Najeriya da kuma wadanda suka kaura daga garuruwansu na yankin Diffa.

Fiye da kashi tamanin cikin dari duk yara ne kanana inji Stephen O'Brien kuma ya cigaba da cewa suna bukatar karin kudade domin su taimakawa 'yan gudun hijiran yadda ya kamata..

Gwamnatin Nijar ta tsara wasu ayyukan tunkarar matsalar domin taimakawa mutanen. Ana bukatar kudi dalar Amurka miliyan dari uku da goma sha shida domin zartas da aikin. To saidai kawo yanzu kashi ishirin da biyar ne na kudin suka shigo hannu.

Dalili ke nan da Stephen O'Brien mataimakin sakataren majalisar dinkin duniya mai kula da ayyukan jin kai yace zai gabatar da wannan bukata a gaban mahalarta taron da za'a gudanar akan 'yan gudun hijira a ranakun ishirin da uku da ishirin da hudu na wannan watan Manyu a birrnin Istanbul na kasar Turkiya domin jan hankalin masu hannu da shuni su bada gudummawar da zata taimaka a shawo kan matsalolin 'yan gudun hijiran yankin Diffa.

Bayanai sun nuna tun a watan Janairun da ya gabata 'yan gudun hijiran na Boko Haram da suke sansanin na yankin Diffa basa samun abincin kosar dasu a kowace rana inda da kyar suke cin abinci sau biyu a wuni

Yau ake kyautata zaton Stephen O'Brien zai isa Najeriya.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG