Accessibility links

Matan Cibok Sunje Majalisar Kasa


Matan Cibok wanda suka kai kukansu Majalisar Kasa a birnin Abuja dake Najeriya, domin bayyana kukan rashin kulawa da neman dalibai da aka sace.

​Mata ‘yan asalin Cibok mazauna birnin Tarayya sunyi tururuwa zuwa Majalisar Kasa sanye da bakaken riguna, inda suka kai kukansu game ‘ya’yansu mata sama da 200 da aka sace a makarantar Sakandare dake Cibok.

Matan sun gayawa Senata Barnabas Gemade wanda ya jagoranci ‘yan uwansa wajen karbansu a harabar majalisar, cewa basu gamsu da yunkurin da gwamnatin Tarayya takeyi ba, wajen kwato daliban ba, domin yanzu sama da mako biyu kennan, babu labarin ‘ya’yan nasu.

Shugaban matan, Madam Naomi Muta tace dasu, da mazajensu basu da sauran dabara shiyasa suka kawo kuka zuwa majalisar.

“Muna nan dai, muna tafiya amma kamar babu rai a jikinmu. Saboda me? ‘Ya’yanmu suna cikin daji kamar dabbobi, bamu san abunda ke faruwa dasu ba. Suna samun abinci su ci? Ka tuna fa an kwashe su da dare, da zani guda a jikinsu. Suna samun ruwa suyi wanka? Suna samun abinci? Suna kwanciya a ina? A cikin daji. Su dauki matakin da ya kamata, su neman mana yaranmu su kawo mana su”, a cewar Madam Naomi.

A lokacin da matan ke jawabi a farfajiyar majalisar, daga cikin majalisar ana muhawara ne, da bada shawarwari, akan mataken da ake gani bangaren zartaswa zai dauka, wajen kwato daliban.

Daliban mata su 234, ‘yan ajin karshe ne dake rubuta Jarrabawar Fita daga Sakandare a Yammacin Afirka, ko WAEC a takaice a lokacin da ‘yan bindiga suka kaiwa makarantarsu farmaki cikin daren Litinin, sama da makonni biyu kennan, inda suka kona makarantar mallakar gwamnati baki dayanta, sannan suka kwashe daliban a cikin manyan motoci suka tafi dasu.

Hukumar tsaron Najeriya, ta bakin kakakinta Chris Olukolade ta fitar da sanarwar ceto kusan duka daliban, kalamun da iyaye da hukumomin makaranta suka musanta, kuma daga baya hukumar tsaron ta janye kalamunta. Ya zuwa yanzu dai bata sake bayanna wani mataki ko daya ba, akan irin aikin da takeyi na gani ta ceto daliban.

Shugaba Jonathan ya gudanar da taro a baya-bayannan da duka gwamnoni, da shuwagabannin al-umma, da hukumomin tsaro game da batun tsaro, inda taron ya kayyade da bayanna matakai da za'a dauka domin kawo karshen rashin tsaro a Najeriya.

Iyaye da ‘yan uwan daliban sun yi kokari da kansu su ceto matan, ta hawa babura sama da 150 domin bin sawun ‘ya’yansu, amma an gargade su akan cewa mutanen da suka sace daliban na dauke da makamai. A farkon makonnan ne kungiyoyin mata da iyayen sun yi taro suna kira a sako daliban. Wasu iyayen ma sun kuduri aniyar suyi zanga-zanga a Cibok domin nuna bacin ransu akan abunda suka kira rashin kulawa da lamarinsu daga hukumomi da jami'ai.

Gwamnatin Jihar Borno tayi alkawarin bada tukuicin Naira miliyan 50 ga duk wanda ya bada wani bayani da zai kai ga ceto yaran mata.

A baya-bayannan ma, Gwamnan daya daga cikin jihohin dake da dokar-ta-baci, wato Jihar Adamawa, Murtala Nyako ya zargi da hannun gwamnati a rincabewar lamuran tsaro a arewarin Najeriya, zargin da gwamnati ta musanta, kuma wasu shuwagabanni a Najeriya da dama suka yi ta sukan gwamna Nyakon. Har yanzu tsohon hafsin rundunar sojin ruwa bai janye kalamunsa ba, wanda a ciki harda tattara shaidu na kaiwa kotun bin kadin manyan laifuka ta kasa da kasa a birnin Hague, domin tuhumar Shugaba Jonathan da kisan kare dangi.

Jihar Borno dai na daya daga cikin jihohin dake fama da tashe-tashen hankula a arewa maso gabashin Najeriya, inda ‘yan bindigar nan da aka fi sani da Boko Haram suke da karfi, wadanda suka fara tayar da kayar baya tun shekara ta 2009. Ya zuwa yanzu gwamnatin Najeriya tace zata shawo kan matsalar, amma kashe-kashen mutane da kone-kone bai tsaya ba.

A kwanakin baya, 'yan siyasa sun bayanna cewa Shugaba Jonathan na so ya sabonta dokar-ta-baci, amma 'yan majalisar na daura dammarar adawa da hakan.

XS
SM
MD
LG