Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Sun Fara Shirin Karbar Mulkin Najeriya a 2023


Matasan Filato
Matasan Filato

Matasa daga sassa daban daban na Najeriya sun gudanar da gangamin karbar mulki daga hannun dattawa.

Yayin da shekara ta 2023 ke kara karatowa, matasa sun dage, inda suka ce suna da lakanin magance matsalolin da kasar ke fuskanta har in sun sami madafun mulki daga hannun wadanda suka ci zamaninsu dana ‘ya’yansu suke kuma cin na jikokinsu.

A hirar su da Muryar Amurka matasan sun bayyana cewa, a shirye suke su kwace mulki a hannun wadannan tsofafin. Bisa ga cewar su, duk cigaban da aka samu a Najeriya, matasa ne suka cimma. Ko a lokacin Shugaba Muhammadu Buhari, da tsohon shugaba Yakubu Gowon da ya hada kan Najeriya kuma ya ja yakin basasa, duk suna cikin kuriciyarsu ne a lokacin.

Karin bayani akan: Muryar Amurka, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

A nasu bangaren, matan da Muryar Amurka ta yi hira da su sun bayyana cewa, zasu goya wa ‘ya’yansu baya don ba matasan damar samad da dama ga mata da matasan Najeriya.

Aishatu Idris Yahuza daya daga cikin matan da Muryar Amurka ta yi hira da su, ta ce dukkan Najeriya daya ne amma matsalolin wariya ya kawo tashe-tashen hankali, shi ya sa ta ke mara wa matasa baya su karbi mulki da karfinsu don a sami cigaba.

A bangare guda kuwa, Hajiya Hauwa Lori da tayi kusan shekaru arba'in ana damawa da ita a harkokin siyasan Najeriya ta ce shawarwarin manya nada muhimmanci.

Saurari cikakken rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

XS
SM
MD
LG