Accessibility links

A dai-dai lokacin da za'a iya cewa jama'ar Najeriya sun fara kosawa da rashin tsaro da ya addabi wasu sassan kasar, abun dubawa anan shine, wani rawa gwamnati ya kamata ta taka game da tsaron mutanenta?

Tsaro na daya daga cikin alhakin da ya rataya akan wuyar gwamnatin Tarayya a kowace kasa ta duniya. Saboda haka a duk lokacin da kasa ta samu kanta a cikin wani halin rashin tsaro, to za’a iya cewa wannan kasar ta rasa komai, saboda rashin tsaro na dakatar da cigaba.

Babu shakka, gwamnatin Tarayya na da bukatar mikewa tsaye, domin ganin cewa wannan matsalar a Najeriya anyi bankwana da ita, domin kuwa kasar nada abinda ake bukata domin tsare duka ‘ya’yanta da dukiyoyinsu.

Sai dai ‘yan Najeriya na cewa gwamnatin Tarayya bata da kowani irin hujja, na bari a cigaba da wannan kashe-kashen da akeyi. Hujjan masu irin wadannan ra’ayoyi shine Najeriya na da wadataccen kudi, haka kuma kasar nada wadatattun masana harkokin tsaro wadanda akayi amfani dasu domin fita daga kangin rashin tsaro a baya.

Kasar Najeriya itace tayi tsayin daka wajen gani an kawo karshen rikicin Saliyo, haka ma itace ta kasa ta tsare, sai da Liberiya ta koma kasa mai walwala. Idan ba’a manta ba, Nejeriya nada hannu wajen gani kasar Kwango ta samu zaman lafiya.

Tambayar anan itace ta yaya matsalar Jihohi wajen uku, ta kasa warware su?

Sashen Hausa na Muryar Amurka ya ji ta bakin Abubakar Tsaf, tsohon kwamishinan ‘yan sandan Jihar Legas, ko babu mafita ne game da wannan matsala?

Abubakar Tsaf yace “abunda yake faruwa a kasar mu yanzu, wato kowa ya saka kudi ne a gaba, da mukami. Babu wanda ya kula da tsaro. Muddin kaje ka basu shawara, sai su ga kamar neman kudi kaje. Babu wanda zai ji ka sam-sam.”

“Idan ba haka ba, munyi magana, munyi magana, munyi zagi babu mai jinmu. To yaya zamu yi? Ya kamata, mutane su tashi su gayawa gwamnati cewa ta kasa,” a cewar Mr. Tsaf.

A shekarun baya, tsohon shugaban Amurka George Bush wanda a zamanin mulkinsa ne aka kai hare-hare da jiragen sama ran 11 ga watan Satumbar 2011, cewa yayi hare-haren aniyar yaki ne ga kasar Amurka, kuma za’a kame wadannan ‘yan ta’adda. Shima tsohon Firayim Ministan Ingila, Tony Blair lokacin da bom ya tashi a kasar Ingila, cewa yayi sai sun kama ko su wanene, kuma an hukunta su bisa doka. Amma Shugaba Jonathan na Najeriya, garzayawa yayi zuwa Kano gangamin siyasa kwana daya da fashewar mummunan Bom a birnin Abuja, da kuma sace dalibai mata a makarantar Sakandare dake Cibok.

Idan ba’a manta ba, bayan hare-haren da aka kaiwa ofishin Majalisar Dinkin Duniya a birin Abuja, Shugaba Jonathan yayi furucin cewa "sauran kasashen duniya na fama da ta’addanci suma, saboda haka Najeriya ma lokacinta ne ta fuskanci nata ta’addancin."

Masu sharhi akan al-amurorin yau da kullum sunce kalamun wadannan shugabanni na nuna kima da kwarewar mulki, amma mutanen Najeriya na cewa gaskiya, doka a Najeriya a fatar baki kawai take, saboda bata aiki akan duk wani wanda ya taka ta.

A kwanakin baya ma, shugaban Najeriya Goodluck Jonathan yace akwai ‘yan Boko Haram a cikin gwamnatinsa, amma har ila yau bai bayanna ko su waye ba. Daga baya kuma, ya fito yace bai san ko su waye ba. Ya zuwa yanzu, ‘yan majalisa basu dauki wani mataki mai karfi ba game da kalamun shugaban kasan ba.

A kwanakin baya gwamnan Jihar Adamawa, Murtala Nyako ya zargi da hannun shugaba Jonathan a lalacewar tsaro a Najeriya, musamman a jihohin dake fama da rigingimu, kalaman da gwamnatin Tarayya ta musanta, amma har ila yau Admiral Nyako bai janye kalamansa ba, kuma ya dauki alwashin tattara takardun shaida domin kai karar shugaba Jonathan a gaban kotun bin kadin manyan laifuka ta kasa da kasa a birnin Hague dake kasar Netherlands, bisa zargin shugaban dan Jihar Bayelsa da kisan kare dangi akan jama'ar arewacin Najeriya.
XS
SM
MD
LG