Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministan Harkokin Zango Ya Fara Rangadi A zangonnin Birnin Accra


Daga Fadama, ministan zai shiga sauran zangonni kamar sabon Zango, Zango lane, Ni’ima, Shukura, Alhamdu, Madina da sauransu.

A lokacin da ya ziyarci sabuwar Fadama, ministan harkokin zango Honarable Abubakar Boniface Sadiqque ya kaddamar da fara rangadin babban birnin Accra, ya kuwa bayyana cewa tun bayan rantsar da shi a matsayin minista ya fara kewayawa yana ganawa da sarakuna da limamen Zango don neman mafita akan matsalolin al’ummar Zango.

Honarable Abubakar Boniface yayi tsokaci akan cewa babu wani abin kirki da gwamnatocin da suka shude suka yiwa jama’ar Zango. Ya ce amma gwamnatin Nana Akufo Addo ta yi alkawarin zata yiwa mutanen Zango abinda zai sa su tuna da ita.

Bayan haka ministan ya ce kudaden da gwamnatin kasar ta ware Cedi miliyan dari biyu da tamanin na gidauniyar raya zango ne, ya kuma gargadi ‘yan zango akan su canza salon siyasar su. Honarable Abubakar ya kuma roki al’ummar Zango akan su dukufa neman ilimi.

Ga krin bayani a cikin sauti daga Ridwan Abbas wakilin sashen hausa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG