Shugaban ya gana da malaman ne a jiya Juma’a, yayin da yajin aikin likitoci ya shiga mako na hudu.
Bayan ganawar sirri da shugabannin kungiyar malaman ta Progressive Teachers Union of Zimbabwe, Emmerson Managagwa bai yiwa manema labarai karin bayani ba.
Wani jami’in kungiyar malaman yace in dai manufar shugaban kasar ne ya samu tabbacin malamai ba zasu yi yajin aiki a lokacin da aka bude makaranta a cikin watan Janairu, to hakarsa bata cimma ruwa ba a wannan zama da suka yi jiya Juma’a.
Malaman suna bukatar a biya su albashi da dalar Amurka ba da kudin kasar ba wanda darajar sa ke kara fadiwa. Haka su ma likitocin Zimbabwe suke bukatar a biya su da dalar Amurka kafin su kawo karshen yajin aikin da suke yi. Sai dai ba batun albashi kadai ne damuwar likitocin ba.
Facebook Forum