Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muhimmancin Mika Mulki Cikin Ruwan Sanyi A Amurka


Shugaba Obama a Berlin

Shugaban Amurka Barack Obama ya jaddada muhimmancin mika mulki "cikin ruwan sanyi" a Amurka, yayinda yake jawabi ga al'umar kasaar Girka yau Laraba kan tsarin demokuradiyya.

"Muna gudanar da zazzafar yakin neman zabe. Amma ko da bayan an kammala zabe, tsarin demokuradiyya ya ta'allaka ne kan mika mulki cikin lumana," inji shugaba Obama a jawabinda yayi a birnin Athens na Girka. Yace babu wai akwai sabanin ra'ayi kwarai da gaske tsakanina d a shugaban Amurka mai jiran gado, amma tsarin demokuradiyyar Amurka ta dara wani mutum daya."
Haka nan shugaban na Amurka mai barin gado ya bayyana goyon bayan Amurka ga turai da kuma tsaronta, yayinda yankin yake bayyana damuwa kan ko shugaban Amurka mai jiran gado saigwammace ya tsame Amurka daga sauran duniya.
Jiya Talata shugaban na Amurka Obama yace kungiyar tsaro ta NATO tana "matukar muhimmanci", kuma tana samarda tabbaci da dorewa ko a lokacinda Amurka take cikin shiri sauya gwamnati.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG