Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mun Ba Buhari Wa'adi Kan Batun Tsaro - Bangaren Adawa


Shugaba Buhari

A ci gaba da cece kucen da ake yi game da tabarbarewar yanayin tsaro a Najeriya, 'yan adawa sun ce sun bai wa Buhari wa'adin kawo karshen aika aikar 'yan ta'adda ko kuma su tsige shi.

Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Phillip Aduda, ya bayyana matsayin ‘yan majalisar ne a ranar Laraba yayin da yake ganawa da manema labarai a zauren majalisar a babban birnin tarayyar kasar, Abuja kamar yadda gidan talabijan na Channels ta ruwaito.

Kafin gabatar da jawabai, ‘yan majalisar daga jam’iyyun adawar sun fice daga zauren majalisar dake zama bayan yin kiran a tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari a zauren majalisar na yau Laraba.

Sanata Aduda ya gabatar da wani batu inda ya nemi shugaban majalisar dattawa, sanata Ahmad Lawan, da ya yi tsokaci a kan batun tsaro a kasar nan da kuma batun tsige shugaba Buhari.

Sai dai Sanata Lawan, wanda ya jagoranci zaman majalisar ya ki amincewa da bukatar shugaban marasa rinjayen jam’iyyar PDP din, yana mai cewa batun tsarin da aka taso bai da tushe balle makama.

Daga bisani bayan fusata da matakin da shugaban majalisar dattawan ya dauka, duk ‘yan majalisar da aka zaba a karkashin inuwar jam’iyyun siyasa ban da jam’iyyar APC mai mulki sun bi sahu su ficewa daga zauren majalisar yayin da zaman majalisar ke ci gaba da gudana.

Batun ficewar na yau dai na zuwa ne a cikin jerin shiga damuwa da ‘yan Najeriya da kungiyoyi daban-daban suka nuna a yayin da matsalar rashin tsaro ke kara ta’azarra a kasar.

Daga farko dai, wani mai rajin kare hakkin bil’adama, Farfesa Chidi Odinkalu, ya soki gwamnatin da shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta kan yadda take tunkarar kalubalen tsaro a kasar.

Sai gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriya, Kungiyar kwadago ta Najeriya da saura kungiyoyi masu fafutukar kare hakkin bil’adama dake ta yin kiraye-kirayen shugaban ya sauya salon yaki da matsalolin tsaron da suka addabi kasar da ma sauran matsaloli kamar a fannin ilimi, yaki da talauci da kuma farfado da komada tattalin arziki da dai sauransu.

A wani bangare kuma, a yau ne kwana ta biyu a zanga-zangar kungiyar kwadago ta Najeriya inda kungiyar ta yi tattaki zuwa majalisar dattawa don nuna rashin jin dadin al’umma agame da yadda gwamnati ke yiwa fannin ilimin kasar rikon sakainar kashi.

Saurari cikakken rahoton Halima Abdulra'uf:

XS
SM
MD
LG