Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Hallaka DPO Da Wasu Jami’an ‘Yan Sanda A Jihar Neja


DPO Umar Muhammed Dakin Gari
DPO Umar Muhammed Dakin Gari

Wasu 'yan bindiga sun hallaka wani babban jami’in ‘yan sanda wato DPO tare da wasu jami’an tsaro guda takwas a jihar Neja dake Arewacin Najeriya.

NIGER, NIGERIA - Rahotanni dai sun tabbatar da cewa maharan dauke da bindigogi akan babura sun aukawa ofishin ‘yan sanda na garin Nasko hedikwatar karamar kukumar Naskon inda suka bude wuta da ya yi sanadiyyar hallaka wannan DPO na ‘yan sandan.

Wani da ya shaida alamarin wanda ya tsallake rijiya da baya a garin na Nasko ya kuma nemi a sakaya sunansa yace sun shiga wani yanayi na tashin hankali.

Yan bindiga
Yan bindiga

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar ta tabbatar da kai wannan mummunan hari, kuma kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Nejan, Monday Bala Kuryas ya ce mutane takwas ne aka kasha aciki harda wasu ‘yan sanda uku tare da wannan DPO Mai suna Umar Muhammed Dakin Gari sauran kuma jami’an tsaro ne na ‘yan banga.

Gwamnatin jihar Nejan dai tayi Allah wadai da kai wannan hari. Sakataren gwamnatin Jihar Nejan Ahmed Ibrahim Matane ya ce kawo lokacin hada wannan rahoto basu kammala bincike akan lamarin ba.

Masu nazari akan sha’anin tsaro dai na ganin wannan tamkar wata ramuwar gayya ce wadannan ‘yan bindiga suka kai bisa la’akari da yadda jami’an tsaro suka fatattaki ‘yan bindigar tare da kashe daruruwansu makonni biyu da suka gabata a jihar Nejan.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari:

‘Yan Bindiga Sun Hallaka DPO Da Wasu Jami’an ‘Yan Sanda A Jihar Nejan Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

XS
SM
MD
LG