Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Myanmar Na Fuskantar Matsin Lamba Kan 'Yan Rohingya


Wasu 'yan kabilar Rohingya da suka tserewa rikicin jihar Rakhine
Wasu 'yan kabilar Rohingya da suka tserewa rikicin jihar Rakhine

Ana ci gaba da nuna matsin lamga ga hukumomin Myanmar kan su ba da kofar da za a kai kayayyakin jin kai ga Musulmi 'yan kabilar Rohingya da ke makale a jihar Rakhine.

Ana ci gaba da zafafa kirayen-kirayen da ake yi ga hukumomin Myanmar, na su ba da kofar da kungiyoyin ba da agajin gaggawa za su kai ga Jihar Rakhine da ke arewacin kasar.

Kiran na zuwa ne sama da wata guda bayan wani hari da ‘yan gwagwarmayar Rohingya suka kai da ya haifar da martanin sojin kasar, wanda ya yi sanadin ficewar Musulmi ‘yan kabilar ta Rohingya su kusan dubu 500 zuwa Bangladesh da ke makwabtaka da Myanmar.

Duk da cewa aksarin Musulmin da ke zaune a jihar ta Rakhine sun fice, akwai rahotanni da ke cewa akwai ragowar wasu da ba a san adadinsu ba, wadanda suka makale, suke kuma cikin mawuyacin halin rashin abinci da magunguna.

Kakakin ofishin Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Myanmar, Pierre Peron, ya ce mutanen na cikin wani mummunan mawuyacin hali, tun bayan da aka tilastawa jami’ansu suka sauya masauki zuwa wani yankin jihar, matakin da ya sa al’amura suka sake dagulewa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG