Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Neman Hanyoyin Warware Rigingimu A Najeriya


Kaduna za ta karbi bakuncin babban taron kasa da kasa na samar da zaman lafiya mai dorewa a Najeriya wanda za a yi a Nuwamba

A cikin watan nuwamba za a yi wani babban taron kasa da kasa a Kaduna da zummar koyon dabarun warware rigingimu daga wasu manyan biranen duniya

Wasu gwamnatoci da kungiyoyi har ma da daidaikun mutane na ci gaba da kokarin kwakulo hanyoyin da suke ganin za a iya bi a magance rigingimun da ke yiwa ci gaban rayuwa barazana a kasar Najeriya.

Daya daga cikin irin wadannan gwamnatoci ita ce gwamnatin jahar Kaduna wadda ta yi amanna cewa babban taron da ake shirin yi a cikin watan nuwamba na manyan biranen duniya da suka taba fama da tashe-tashen hankula da rigingimu amma suka samu hanyoyin ganin bayan su, zai taimaka matuka wajen samar da zaman lafiya mai dorewa.

Wakilin Sashen Hausa a jahar Kaduna Isah Lawal Ikara ya na da karin bayani a cikin wannan rahoto.

Kaduna na shirin yin babban taron kasa da kasa akan warware rigingimu - 1:46
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:46 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG