Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sanata Yace Tilas A Zakulo A Hukumta Wadanda Suka Kashe Dalibai


Dakarun Najeriya

Sanata Alkali Abdulkadir Jajere, daga Yobe, yace abin takaici ne yadda har yanzu aka kasa zakulo marasa imanin da suka yi ma dalibai kisan kiyashi.

Wani bdan majalisar dattijan Najeriya daga Jihar Yobe, yace tilas duniya ta yi Allah wadarai da kisan kiyashin da 'yan bindigar da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne suka yi ma dalibai a cikin Jihar ta Yobe ba sau daya ba, ba sau biyu ba.

Sanata Alkali Abdulkadir Jajere, mai wakiltar Yobe ta Kudu a majalisar dattawan Najeriya, yace abin takaci ne cewa har yanzu ba a damko wadannan 'yan bindigar an kuma yi musu hukumcin da ya kamata da irin wannan danyen aiki na rashin imani da suka yi ba.

Sanatan yayi misali da harin bam da aka kai lokacin gudun famfalaki a garin Boston na Amurka, inda hukumomi ba su tsaya ba sai da suka zakulo wadanda suka aikata wannan abu.

Yace dole ne abi kadin wadannan dalibaui na kolejin koyon aikin gona ta Jihar Yobe dake Gujba da 'yan makarantar sakandare ta Mamudo da aka kashe cikin ruwan sanyi a Jihar.

A hirarsa da VOA Hausa, Sanata Alkali Jajere yace da mamaki idan an tura sojojin Najeriya aikin kiyaye zaman lafiya a wasu kasashe, har lambar yabo suke samu, amma sun kasa shawo kan wannan lamarin na 'yan Boko haram a Najeriya. Yace tilas ne su tsara sabbin dabarun takalar 'yan bindigar da sun koma daji a saboda hadin kan da jama'a suke ba hukumomin tsaro a yanzu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG