Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane A Jihar Adamawa


Motocin da aka kone

Wasu 'yan bindiga sun kai hari a wani kyauye cikin jihar Adamawa dake kusa da iyaka da jihar Borno

Kwanana kwanan nan al'ummar Adamawa ke murnar samun zaman lafiya da fatan gwamnatin tarayya zata cire masu dokar ta bacin da ta kakaba mata sai gashi wasu 'yan bindiga sun kai hari a wani kauyen jihar dake kan iyaka da jihar Borno, jihar da 'yan Boko Haram suka sake tayar da karin baya cikin watanni biyun da suka gabata.

Sanadiyar harin da wasu 'yan bindiga suka kai kan kauyen Itoko a karamar hukumar Madagali dake makwaftaka da jihar Borno yanzu jama'ar jihar Adamawa suna zaman dar dar da rashin tabbacin ko menene ka iya faruwa nan gaba. Kamamr yadda ganau ya tabbatar an samu asarar rayuka da dama a harin kuma wasu da yawa sun jikata. Wani mutumin garin ya ce mutane takwas aka kashe kana goma sha shida aka raunata. Mutanen garin suna tserewa suna shiga daji. Babu wanda ke cikin gidansa kawo yanzu domin duk sun arce. Sojoji dake garin da aka gaya masu basu kula ba sai da gari ya waye. To amma kakakin sojojin dake Yola ya ce babu cikakken labari kan lamarin da ya faru.

Duk da abun da ya faru sojoji sun ce suna samun nasara domin suna tare hanya, suna bincike, suna kama 'yan kungiyar Boko Haram.

Ga karin rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG