Accessibility links

An Kashe Mayakan Boko Haram 15 A Jihar Borno


Sojoji masu sintiri a kusa da gidan telebijin na NTA a Maiduguri

Shiyya ta 7 ta sojojin Najeriya dake Maiduguri ta ce ta yi gumurzu da tsageran Boko Haram a Damboa wadanda suka kai hari suka kashe farar hula 5 kafin a fatattake su

Sabuwar shiyya ta 7 ta mayakan Najeriya mai hedkwata a Maidugurin Jihar Borno, ta ce ta kashe mayakan kungiyar Boko haram su 15, yayin da ta kwace muggan makamai da dama a wani ba-ta-kashin da suka yi a garin Damboa, wanda ke tsakiyar dazuzzukan da aka yi imanin tsageran sun buya ciki.

Rundunar ta ce 'yan bindigar Boko Haram sun kai farmaki kan garin Damboa ranar asabar da asuba, da misalin karfe 4:30, inda suka far ma wasu mutanen dake shirin zuwa sallar asuba. 'yan bindigar sun kashe mutane 5, suka kona gidan hakimin Damboa, sannan suka cunna wuta a wasu kantunan jama'a dake kusa da nan.

'Yan bindigar sun yi arangama da sojoji kafin su gudu, inda aka kashe 15 cikinsu, wasu kuma suka tsere cikin daji suka bar makamansu har ma da wata motar a-kori-kura.

Sanarwar da kakakin shiyya ta 7 ta rundunar sojojin Najeriya, Kyaftin Aliyu Danja, ya raba wa 'yan jarida ta ce an samu albarusai masu yawa da bindigogi kirar AK-47 guda biyar, da makaman cilla roka ko gurneti. Sanarwar ta yabawa mutanen garin Damboa a saboda hadin kan da suke ba jami'an tsaron dake kokarin kawo karshen wannan fitina ta 'yan Boko Haram a yankin.

Ga cikakken rahoto daga bakin Haruna Dauda a Maiduguri.

XS
SM
MD
LG