Accessibility links

Tawagar Gwamnatin Adamawa Ta Ziyarci Wadanda Aka Kai Musu Farmaki

  • Garba Suleiman

Wasu daga cikin mazauna garin Madagali sun bayyana yadda suka yi da 'yan bindigar da suka ce yanka su zasu yi, ba zasu harbe su ba.

Wata tawaga ta gwamnatin Jihar Adamawa ta ziyarci mutanen da wasu 'yan bindigar da ake kyautata zaton na Boko haram ne suka kai musu farmaki har suka kashe mutane da dama, domin jajanta musu tare da kai musu tallafi.

Kakakin majalisar dokokin Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru, yace yana rokon kada Allah ya sake nuna musu irin wannan abin bakin ciki da koma-baya da kuma nuna rashin imani.

Wani mutumin garin Bindiki inda aka kai harin, ya bayyanawa wakilin sashen Hausa, Ibrahim Abdulaziz, inda 'yan bindigar suka yi kokarin yanka shi, da yadda yayi ta rokonsu a kan su harbe shi ya mutu maimakon su yanka shi. Yace dansa ya taimaka masa wajen ganin ya samu kubuta da ransa daga hannun wadannan mahara.

Kwamishinan harkokin kan iyaka na Adamawa, Alhaji Haruna Bello, yace gwamnan Jihar, Murtala Nyako, ya nada kwamitin da zai taimaka ma mutanen da suka fuskanci wannan ukuba ta 'yan bindigar, kuma nan ba da jimawa ba za a kai musu tallafin da ya dace.

Da yawa daga cikin mutanen garin dai, sun yi rokon da a taimaka a kara karfafa tsaro, ta hanyar girka karin ja mi'an tsaro a wannan yanki nasu.

XS
SM
MD
LG