Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NEJA: Dalibai Shida Daga Cikin 136 Da Aka Yi Garkuwa Da Su Sun Mutu


Shida daga cikin dalibai 136 da aka yi garkuwa da su daga wata makarantar Islamiyya da ke jihar Neja a arewa maso tsakiyar Najeriya sun mutu sakamakon rashin lafiya, kamar yadda shugaban makarantar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ranar Litinin.

Yan bindigan da suka yi garkuwa da daliban sun nemi kudin fansa don sakin daliban, wadanda aka yi garkuwa da su a watan Mayu bayan da wasu gungun masu dauke da makamai akan babura suka kai hari makarantar a garin Tegina.

Ana zargin gungun yan bindiga masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa da kai jerin hare -haren kan makarantun kwana a arewacin Najeriya inda suka sace dalibai sama da 1,000 tun watan Disamba.

Shugaban makarantar, Abubakar Garba Alhasan, ya ce masu garkuwar sun kira ne don su shaida mashi cewa yaran sun mutu ne sakamakon rashin lafiya sannan kuma sun bukaci a biya kudin fansa.

Abubakar Adam, wanda ‘yan kungiyar ke rike da‘ ya’yansa bakwai, ya ce masu garkuwar sun kira shugaban makarantar don neman kudin fansa.

Masu garkuwa da mutane a ranar Lahadin da ta gabata sun saki wasu dalibai 15 da aka dauka a watan da ya gabata daga wata makarantar Baptist a arewa maso yammacin Najeriya, bayan da iyaye suka biya kudin fansa da ba a bayyana ba don kubutar da su.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a watan Fabrairu ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da su daina biyan masu garkuwa da mutane.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG