Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Neja: ‘Yan bindiga Sun Kashe Mutum Biyu, Sun Yi Garkuwa Da Shugaban Jam’iyyar APC


Gwamna Abubakar Sani Bello, yayin da yake bayani kan muhimmancin samar da 'yan sintiri a wani taro na daban (Twitter/Gwamnatin Neja)
Gwamna Abubakar Sani Bello, yayin da yake bayani kan muhimmancin samar da 'yan sintiri a wani taro na daban (Twitter/Gwamnatin Neja)

Wasu 'yan bindiga sun hallaka akalla mutum biyu tare da jikkata wasu da dama, da kuma yin garkuwa da shugaban jam'iyyar APC na yankin Arewacin jihar Neja a Najeriya.

‘Yan bindigan dai sun fara kai hari ne a kauyen Karen Bana inda suka fara kashe mutum biyu tare da jikkata wasu da dama da kuma yin awon gaba da wadansu.

Sannan daga bisani suka isa garin Bobi inda suka yi awon gaba da shugaban jam'iyyar APC na yankin Arewacin jihar Neja Alhaji Aminu Bobi alokacin da yake gonarsa.

A cewar wani Malam Halliru Sani, ‘yan bindigan sun kashe mahaifinsa da kuma ‘ya’yansa a lokacin harin Karen Banan.

Ya Zuwa lokacin hada wannan rahoto dai babu wani karin haske daga rundunar ‘yan sandan jihar Nejan akan wannan hari domin kokarin samun kakakin ‘yan sandan jihar DSP Wasiu Abiodun ya ci tura.

Amma gwamnatin Jihar Nejan ta tabbatar da aukuwar lamarin, dama kokarin da ta ce tanayi dan kubutar da shugaban APC a cewar sakataren gwamnatin Jihar Nejan Alhaji Ahmed Ibrahim Matane.

Wannan dai yana zuwa ne a daidai lokacin da daliban makarantar Islamiyyar Salihu Tanko su kimanin 148 suka haura makonni tara a hannun ‘yan fashin dajin.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari:

Neja: ‘Yan bindiga Sun Kashe Mutum Biyu, Sun Yi Garkuwa Da Shugaban Jam’iyyar APC
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00


XS
SM
MD
LG