Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Na Bukatar Taimakon Kasar Faransa


SHUGABA MUHAMMADOU ISSOUFOU
SHUGABA MUHAMMADOU ISSOUFOU

Kasar Nijar da kawayenta na yankin Sahel, na bukatar goyon bayan kasar Faransa, don shawo kan kasashen duniya wajan samar da kudaden gudanar da rundunar hadin gwiwa

Ministan harkokin wajen kasar Faransa Jean Yves Ledrian, ya kai ziyara a jamhuriyar Nijar, inda ya tattauna da hukumomin kasar akan maganar karfafa hulda dake tsakanin kasashen biyu musamman a wannan lokaci da batun tsaro da matsalar bakin haure ya dauki hankalin duniya.

Mahauwara akan matsalolin da yau ake dauka tafkar mafarin matsallar tsaro da kwararan bakin hauren dake zama karfen kafa ga duniya baki daya sh ne makasudin ziyarar Ministan harkokin wajen kasar Faransa Jean Yves Ledrian, kamar yadda Ministan harkokin wajen kasar Nijar, Alhaji Ibrahim Yakuba, ya bayyana.

Domin tantance irin kalubalen da gwamnatin Nijar, ke fuskanta na samarda ilimi, ga yaran kasar, Ministan na harkokin wajen Faransa, ya ziyarci makarantar Firamare Madina ta uku, dake cikin jerin makarantun dake baiwa dalibai karatu cikin harsunan gida hade da Faransanci dake birnin Yamai, abinda Ministan harkokin wajen Faransa ya ce yana bisa turba domin hakkan zai taimaka samarda ilimi mai inganci.

Akan maganar tsaro Nijar, da kawayenta na kungiyar kasashen da suka kafa rundunar hadin gwiwa domin yake da ta’addanci a yankin Sahel, na bukatar goyon bayan Faransa, don shawo kan kasashen duniya na samarda kudaden gudanar da rundunar ta hadin gwiwa.

A cewar Jean Yves Ledrian, faduwa taso dai dai da zama domin kasar Faransa ce ke shugabancin kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya a halin yanzu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG