Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Ta Mikawa Najeriya Mutum 22 Da Ke Kokarin Tsallakawa Kasashen Ketare


A Najeriya masana na ganin cewa halin kuncin rayuwa da jama'a ke fuskanta na daya daga abubuwan da ke saka su jefa rayukan su cikin hadari ba tare da la'akari da illolin da abin zai haifar ba.

Wannan na zuwa ne lokacin da Jamhuriyar Nijar ta tuso keyar ‘yan Najeriya wadanda suka ratsa kasarsu zuwa kasashen ketare don neman saukin rayuwa.

Wannan karon ma matasa ne mata 21 da namiji daya da suka fada irin wannan tarko aka damke a Jamhuriyar Nijar bayan sun shiga kasar ta iyakar Illela da ke garin Sakkwato, kuma mahukunta kasar ta Nijar suka mayar da su Najeriya.

Yawan yekuwar da hukumomi da kungiyoyi masu zummar karewa da kyautata rayukan ‘yan Najeriya ke yi akan illolin fadawa tarkon masu safarar mutane na tashi a banza domin matsalar ta ki ja da baya a kasar.

A can baya an yi ta samun rahotanni na kama mutane da ake tuhumar an yi safarar su a sassa daban-daban musamman jihohin da ke da iyakar da wasu kasashe irin Sokoto.

Barrister Abubakar Bashiru, kwamandan yanki na hukumar hana safarar bil'adama shiyar Sokoto, ya ce sun karbi wasu mutane da aka yi safarar su don kokarin fita da su kasashen ta Nijar zuwa Libya da kuma kasashen Turai.

Mutanen su 22 kuma duka ‘yan Najeriya ne a cewarsa.

Akasari dalilian wadanda suka fada wannan tarkon ana masu alkawarin za'a nema masu aiki ne a kasashen ketare, a cewar su.

A cewar wata daga cikinsu, kawar ta ce ta gayyace ta zuwa birnin Tripoli a kasar Libya ta yi aiki. Wata kuma ta ce a dandalin sada zumunta na WhatsApp ta ga bayani cewa idan ta je Sokoto akwai tsammanin za ta samu aiki.

Masana halayyar dan Adam irinsu Farfesa Tukur Muhammad Baba, na ganin cewa akwai dalilai dake kawo samun hakan.

Irin wadannan mutanen idan har suka samu nasarar tsallakewa idan suka dawo Najeriya akwai yiwuwar su zo da munanan halaye da suka koya a can kasar da suka je.

Ko bayan hakan samar da ayukkan yi ga ‘yan kasa kan iya taimakawa ga ceto su daga fadawa irin wannan tarko.

Saurari rahoto daga Muhammadu Nasir:

Nijar Ta Mikawa Najeriya Mutum 22 Da Ke Kokarin Tsallakawa Kasashen Ketare
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00


Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG