Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obama Ya Yiwa Wadanda Suka Rasa 'Yanuwa A Orlando Ta'aziya


Shugaba Obama da Mataimakinsa Biden suna ajiye fure wajen da aka kashe mutane 49 kana aka jikata wasu 53 a garin Orlando

Shugaba Obama ya gaggauta shirya kai ziyara zuwa Orlando, a jihar Florida, bayan kashe mutanen da aka yi a gidan rawa.

Wannan shine karo na 10 da shugaban ya ziyarci inda akayi harbin da aka kashe mutane, domin yayi ta’aziya, kana ya nuna alhinin sa ga ‘yan uwan wadanda wannan lamari ya rutsa dasu.

Ko a jiya Alhamis sai da shugaba Obama ya samu kansa a cikin irin wannan yanayi na matsayin uba dake cikin jimamin wadanda aka kashe sailin da yake ganawa da ‘yan uwan wadanda aka halbe a Orlando. A kissa mafi muni a tarihin Amurka da yayi dalilin mutuwar mutane 49 kana wasu 53 suka samu rauni.

‘Yan uwan wadanda suka taba samun kansu cikin irin wannan yanayi wani lokaci can baya suka ce babban abinda suka fi tunawa shine irin kalaman alhinin da shugaban yayi musu.

Ko a wannan karon ma sai da shugaban ya maimata ire-iren wadannan kalaman a garin Orlando.

Shugaba Obama yace “wani lokaci can baya nayi wadannan kalamai ga ‘yan uwa da iyayen wadanda irin wannan al’amari ya rutsa dasu, amma kuma wasu suna tambaya ta, kome yasa irin hakan ke ci gaba da faruwa?. Wadannan mutanen sun bukaci mu kara kaimi wajen ganin mun dakile aukuwar wannan mummunar tarbiya, suka ce basu damu da siyasar dake tattare da yin hakan ba wanda ni ma na yadda da haka”.

Sai dai kafin ma yakai wannan ziyarar mai magana da yawun Fadar White House din Josh Earnest yace shugaba Obama na kallon wannan ziyara a matsayin wata babbar abu ce da ya zame wajibi a yi ta

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG