Accessibility links

Oyo: Tsoffin Ma'aikata Sun Fantsama cikin Zanga-zangar Neman Hakkinsu


Ma'aikata suna zanga-zanga

Daruruwan tsoffin ma'aikatan jihar Oyo suka fantsama cikin zanga-zangar jawo hankalin gwamnatin jihar ta biyasu kudin fansho da yanzu an yi wata da watanni ba'a biya ba

Ma'aikatan sun shirya zanga-zanga din zuwa fadar gwamnatin jihar inda suka mika kukansu.

Ma'aikatan sun shiga zanga-zangar ne bayan kwanaki bakwai da suka baiwa gwamnatin ta biyasu hakkinsu suka wuce ba tare da an biya masu bukatunsu.

Yayinda yake jawabi mataimakin shugaban kungiyar 'yan fansho ta reshen jihar Oyo Mr. Gbade Akande yace gwamnatin jihar Oyo ta yi biris dasu. Yace suna shan wahala cikin jama'ar kasar saboda ba'a biyan 'yan fansho hakkokinsu kan lokaci.

Yace hakkokin da suke nema halalinsu ne wadanda kundun tsarin mulkin Najeriya ya amince dasu.

Shi ma mataimakin shugaban 'yan afnsho na kasa Alhaji Latif Adegoke ya roki gwamnan jihar Oyo Abiola Ajimobi da ya biyasu duka hakkokinsu. Ya roki gwamnan jihar ya yiwa Allah da Annabi Isa alehi-salam ya biyasu hakkokinsu gaba daya.

Gwamnan ta bakin mataimakinsa Moses Adeyemo yace ba da gangan ba ne suka ki biyan tsoffin ma'aikatan kudin fansho. Yace rashin biyansu ya ta'allaka ne akan rashin samun isasshen kudi daga gwamnatin tarayya. Ya bukacesu da su kara yin hakuri.

Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal.

XS
SM
MD
LG