Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistabn Ta Bukaci Sulhu Tsakaninta Da India


Firai ministan Pakistan, Imran khan and Narendra Modi na India
Firai ministan Pakistan, Imran khan and Narendra Modi na India

Firai Ministan Pakistan Imran Khan ya aikawa takwarar aikinsa na India Narendra Modi da wasikar dake kira ga shirya zaman sasantawa tsakanin su.

A cikin wasikar da aikawa Modi a ranar Juma’a, ya masa barka game da zabensa a karo na biyu a matsayin Firai minista. Khan ya rubuta cewa Pakistan tana so a magance duk wata matsala, ciki har da batutuwa masu nasaba da takaddamar yankin Kashmir, a cewar kafofin yada labarai.

Khan ya kara da cewa tattaunawa tsakanin kasashen biyu, itace hanya daya tilo da zata taimakawa kasashen su yaki talauci, a don haka dole ne su yi aiki tare domin ci gaban yankin.

Pakistan tana bukatar tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a yankin Asia ta Kudu a cewar wasikar Khan, yana mai fadin cewa dole ne a samu haka kafin kasashen da ma yankin su ci gaba.

Sai dai jami’an India sun ce Modi bai shirya wata ganawa da Khan a taron kolin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Turai da Asia a Bishkek babban birnin kasar Kyrgyzstan a mako mai zuwa.

A iya sani na babu wata ganawa da aka shirya tsakanin Firai Minista Modi da takawarar aikinsa na Pakistan Imran Khan a gefen taron kolin, inji mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen India, Raveesh Kumar.


A ‘yan shekaru da suka shude, India taki amincewa da duk wani shirin tattaunawa, tana mai cewa sai an kawo karshen ta’addancin kan iyaka kafin fara wata tattaunawa.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG