Ministan tsaron kasar Pakistan, ya ce akwai yiwuwar a samu kyakkyawar danganta tsakaninsu da abokiyar hamayyarsu India, yana mai nuni da yadda shugabannin kasashen Korea ta Arewa da ta Kudu suka kafa tarihi, bayan wata haduwa da suka yi.
Amma ministan tsaron, Khurram Dastgir, ya ce akwai bukatar a samu girmamawa ta fuskar siyasa da kuma kwarin gwiwar da zai sa a manta da abinda ya faru a baya.
A wata hira ta musamman da ya yi Muryar Amurka, Ministan na Pakistan, ya nanata yadda ta da jijiyar wuya ta fuskar diplomasiyya da ta fuskar soji da ake samu kan yankin Kashmir, ya kara nuna cewa akwai yiwuwar cewa takaddamar da ake yi akan yankin na Himalaya, zai iya zama wani yanki da zai iya ruruta wutar rikici tsakanin kasashen biyu da ke nahiyar Asiya, wadanda dukkansu suka mallaki makamin nukiliya.
Kusan a cikin kowane mako, dakarun kasashen biyu sai sun yi musayar wuta a shingen da ya raba dukkaninsu da kan iyakar yankin na Kashmir.
Dukkaninsu kuma kan zargi juna da haddasa wannan mummunan fitna, kuma kowa ya kan yi ikrarin cewa yankin nasa ne.
Yankin na Kashmir ya haddasa yake-yake har sau uku a tsakanin kasashen biyu, tun bayan da kowanensu ya samu ‘yan cin kai daga Birtaniya a shekarar alif-dari-tara-da-arba’in-da-bakwai.
Facebook Forum