Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP Ta Ce Wadanda Suka Sauya Sheka Basu Da Wani Tasiri


Ganawar Shugaba Muhammadu Buhari Da Sanata Saidu Umar Kumo
Ganawar Shugaba Muhammadu Buhari Da Sanata Saidu Umar Kumo

Biyo bayan sauya sheka da wasu manyan ‘yan PDP ciki har da tsoffin shugabannin jam’iyyar na kasa da na arewa zuwa APC mai mulki, PDP ta ce hakan rabuwa da rakai ne kuma mutanen ba su da wani tasiri

Sakataren PDP Sanata Umar Tsauri, ya baiyana haka a martanin sa ga batun sauya sheka da APC ke cewa alamu ne da faduwar adawa a zaben watan gobe.

APC ta bakin babban sakataren jam’iyyar Mai Mala Buni ta yi maraba da sauya shekar a matsayin babbar riba ga jam’iyyar da nuna irin tsohon shugaban PDP na arewa Sanata Babayo Gamawa ba rakai ba ne ga kowacce jam’iyya.

Daya daga wadanda su ka sauya shekar shi ne jagoran kamfen na Atiku a neman tikiti na arewa maso gabas Sanata Saidu Umar Kumo, ya ce PDP kullum na daukar sa tamkar bako.

An ga hoton shugaba Buhari da Sanata Kumo a fadar gwamnati su na ganawa wanda kusan shi ne karo na farko tun babewar su a 2007 zamanin mulkin Umaru ‘Yar Adua.

Ganawar Shugaba Muhammadu Buhari Da Sanata Saidu Umar Kumo
Ganawar Shugaba Muhammadu Buhari Da Sanata Saidu Umar Kumo

Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG