Rashford dan shekaru 22, ya yi fafutukar ganin gwamnatin Britaniya ta ci gaba da baiwa yara ‘yan makaranta abinci, kusan su miliyan 1.3, a lokacin hutun zaman gida na annobar coronavirus.
A cewar masarautar ta Britaniya, Rashford ya taka muhimmiyar rawa wajen fafutukar neman gwamnati ta dawo ta ci gaba da ciyarwar bayan ta dakatar da tsarin sakamakon barkewar annobar COVID-19.
Dan wasan ya rubuta wasika zuwa ga Prime Ministan Britaniya, yana mai bayyana irin halin da shi kan sa ya fuskanta sakamakon ya tashi ne a cikin iyali masu karamin karfi, da kuma yadda samar da abincin ga yara ‘yan makaranta ya ke da matukar muhimmanci wajen karfafawa iyalai masu karamin karfi.
Haka kuma Rashford bai tsaya nan ba, domin ko shi ma ya kafa gidauniya da ta tara kudi fiye da fam miliyan 20, inda ya samar da karin shirin ciyar da yara dake cikin iyalai masu karamin karfi, ta hanyar hadin gwiwa da gidajen sayar da abinci.
Duk da yake Rashford ya bayyana matukar farin ciki da samun wannan matsayin daga masarautar ta Britaniya, to amma ya ce yana ganin yanzu ne ma ya soma fafutukar da yake son cimma makasudi.
Facebook Forum