Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Real Madrid Ta Taya Mbappe Miliyan 137


Kylian Mbappe
Kylian Mbappe

Mbappe ya ci wa PSG kwallaye 133 ya kuma taimaka aka ci wasu 63 a wasanni 174 da ya buga a zamansa a kungiyar.

Real Madrid ta taya dan wasan Paris Saint Germain Kylian Mbappe akan fam miliyan 137.

Dan shekara 22 Mbappe na da kasa da shekara daya kwantiraginsa yak are a Paris.

Rahotanni sun ce kungiyar ta PSG ta sha neman Mbappe ya sabunta kwantiragin nasa amma ya ki, inda rahotanni ke cewa dan wasan kan ce burinsa shi ne, ya taka leda a Madrid.

Duk da cewa PSG ta yi nasarar yin cefanen Lionel Messi daga Barcelona, Mbappe ya fito karara yana cewa ya fi son ya koma gasar ta La Liga.

Bayanai sun yi nuni da cewa a ranar Lahadi Real Madrid ta mika tayinta, amma PSG ba ta amsa mata ba har ya zuwa lokalin hada wannan rahoto.

An dai kwashe watanni ana alakanta Mbappe dan asalin kasar Faransa da kungiyar ta Madrid duk da cewa kungiyar ta tafka asarar euro miliyan 300 saboda annobar coronavirus.

Mbappe ya ci wa PSG kwallaye 133 ya kuma taimaka aka ci wasu 63 a wasa 174 da ya buga a zamansa a kungiyar.

A karshen makon nan mai zuwa Messi zai fita wasansa na farko ga sabuwar kungiyarsa ta PSG inda za su kara da Reims.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG