Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Jihar Warrap A Sudan Ta Kudu Yana Lakume Rayuka


Sudan ta Kudu
Sudan ta Kudu

Fiye da mutane 70 aka kashe, sannan da dama suka jikkata a wata arangamar da ta shafi sojoji da fararen hula a jihar Warrap a Sudan ta Kudu a karshen makon nan, in ji jami'an yankin da jami’an majalisar dinkin duniya.

Kakakin majalisar dinkin duniya Stephane Dujarric ya fada a jiya Talata cewa, Ofishin jinkai na majalisar dinkin duniya a Sudan ta Kudu (UNMISS) ya karbi rahotannin wadanda suka mutu daga hukumomin yankin Tonj East County.

"Rikicin ya samo asali ne sakamakon rashin jituwa kan wani shiri na yankin," in ji shi. “A yayin artabun, an ba da rahoton sace kayayyakin kasuwa da ke garin Romic, sannan an kone wasu shaguna kurmus. Mata da yara da yawa sun gudu saboda tsoron rayukansu.”

Dujarric ya ce, rundunar kiyaye zaman lafiya ta MDD. tana kan hanyarta ta zuwa yankin don tantance yanayin tsaro.

Daraktan zartarwa na gundumar Tonj East County, Makuei Mabior, ya shaidawa shirin South Sudan in focus na Muryar Amurka cewa, wata takaddama ta barke tsakanin wasu gungun matasa da sojoji a kasuwar Romic, bayan wani sojan ya umarci wani saurayi ya cire wani jan mayafi daga kansa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG