Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Romelu Lukaku Ya Tafi Jinya


Dan wasan Belgium/Chelsea Romelu Lukaku yana dingisawa a lokacin da ya ji rauni (AP)

A ranar Laraba Belgium za ta kara da Poland sannan ranar Asabar ta kara da Wales, amma dan wasan na Chelsea ba zai buga duka wasannin ba in ji Martinez.

Dan wasan gaba na kasar Belgium Romelu Lukaku ba zai buga wasanni biyu na gaba ba a gasar Nations league, bayan wani rauni da ya samu a agararsa, mai horar da 'yan wasan Roberto Martinez ya fada a ranar Talata.

Lukaku ya ji ciwon ne a karawar da suka yi da Netherland kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

A ranar Laraba Belgium za ta kara da Poland sannan ranar Asabar ta kara da Wales, amma dan wasan na Chelsea ba zai buga duka wasannin ba in ji Martinez.

Belgium ta sha kaye a hannun Netherland a karawar da ci 4-1 a Brussels.

Sai dai Martinez ya ce raunin “bai yi muni ba” kamar yadda aka yi fargaba a baya.

“Akwai matukar wuya, idan zai buga wasanmu na karshe.” Martinez ya ce.

Dubi ra’ayoyi

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG