Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Abia Ta Ce Bata Da Masaniyar Inda Nnamdi Kanu Ya Ke


Rundunar 'yan sandan jihar Abia, ta bayyana cewa bata da wata masaniya akan inda madugun kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu yake a halin yanzu da ake ci gaba da tofa albarkacin baki a kan batun a kudancin Najeriya.

A wata hira da suka yi da wakilin sashen Hausa na muryar Amurka, Alphonsus Okoroigwe, Kwamishinan rundunar 'yan sandan jihar Abia, Mr Anthony Okwueze, ya bayyana cewa basu da masaniya akan inda Nnamdi kanu yake.

Jami'in ya bayyana cewa da suna da masaniya da sun fahimtar da shi akan tunani mai armashi, dan haka ya kara da cewa idan manema labarai na da masaniya, akwai bukatar su shaidawa jami;an domin tafiya tare wajan shawo kan lamarin.

Lamarin batan dabon da madugun kungiyar ya yi ya haifar da musayar ra'ayoyi a tsakanin jama'ar jihar, Mr Moses Okoye, wani dan kasuwa ne kuma ya bayyana cewa tana iya yiwuya Nnamdi Kanu na raye ko kuma baya raye ganin yadda sojoji suka kai hari a fadar mahaifinsa, dan haka idan yana raye a taimaka a sake shi.

A cewar Mr Emeka, wani daga cikin mazauna birin ya bayyana cewa a nasa ra'ayin shugaban kungiyar na nan a raye domin a cewar sa da anga gawar sa a ranar da sojoji suka kai hari a fadar mahaifin sa.

Saurari rahoton Alphonsus domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:13 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG